Yawan kudin da kasar Sin ta kasafta ta fannin tsaro zai kai kimanin yuan biliyan 1000
Wani jami'in ma'aikatar harkokin kudi a kasar Sin, ya bayyana a yau Litinin cewa, yawan kudin da kasar Sin za ta kasafta ta fannin tsaro a wannan shekara, zai kai kimanin yuan biliyan 1044 da miliyan 397, adadin da ya karu da kashi 7% idan aka kwatanta da na bara. Jami'in ya bayyana haka ne a yayin da yake tattaunawa da 'yan jarida dangane da kasafin kudin tsaron kasar a wannan shekara.
A daya bangaren kuma, yayin taron manema labarai da aka kira a Asabar da ta gabata dangane da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kakakin taron, Madam Fu Ying ta bayyana cewa, duk da cewa kudin da aka kasafta a fannin tsaro a shekarar 2017 zai karu da 7%, amma yawan sa bai wuce kimanin kashi 1.3% na alkaluman ma'aunin tattalin arziki wato GDP na kasar ba. Kuma hakan ya kasance a wannan matsayi cikin shekaru.(Lubabatu)