Kakakin zaman majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin CPPCC da za a bude a gobe Mr. Wang Guoqing, ya ce akwai hasashen tattalin arzikin kasar Sin na bana, zai ci gaba da zama jigo, na bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya.
Mr. Wang wanda ke bayyana hakan yayin wani taron 'yan jaridu da aka gudanar a Alhamis din nan, ya ce a bara tattalin arzikin Sin ya karu da kaso 6.7 cikin dari, wanda hakan ke nuna kyakkyawan fata na cimma nasarar shirin raya kasar na shekaru biyar biyar karo na 13, wanda kasar ta sanya gaba.
Wasu alkaluma da bankin duniya ya fitar sun yi hasashen cewa, a bara bunkasar tattalin arzikin Sin na kan gaba, da kusan kaso daya cikin uku na daukacin ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda shi ne a sahun farko tsakanin ragowar kasashen duniya.(Saminu Alhassan)