in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping: Sin ba za ta rufe kofa ga kasashen ketare ba
2017-03-06 10:38:02 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin za ta tsaya kan manufar samar da ci gaba, da zurfafa yin gyare-gyare a cikin gida, da bude kofa ga kasashen ketare, kana da karfafa karfin takara, da nufin gaggauta raya manyan biranen zamani bisa tsarin gurguzu.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, bayan ya saurari jawabin da wakilan kungiyar Shanghai suka gabatar, wadanda ke halartar zaman taro karo na 5 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12.

Xi ya kara da cewa, kafa yankin cinikayya maras shinge, wani mataki ne bisa manyan tsare-tsare da Sin ta dauka, na zurfafa gyare-gyare, da habaka bude kofa ga kasashen ketare bisa sabon yanayin da ake ciki.

A cewarsa Sin ba za ta rufe kofa ga kasashen ketare ba, a maimakon haka za ta karfafa wannan aiki a dukkan fannoni.

Xi ya bayyana fatan sa, na ganin birnin Shanghai ya samu sabuwar nasara wajen yin kwaskwarima kan yankin ciniki maras shinge, da raya cibiyar kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da kuma gudanar da harkokin al'umma da na jam'iyyar Kwaminis ta Sin.

Baya ga haka Xi ya ce a matsayinsa na wani abin koyi, ya kamata birnin Shanghai ya nemi wata sabuwar hanyar gudanarwa, wadda za ta dace da halin musamman na babban birni, wannan dai muhimmin batu ne dake shafar bunkasuwar birnin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China