in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasafin kudin tsaron kasar Sin zai karu da kimanin kashi 7% a shekarar 2017, adadin da ya ragu idan aka kwatanta da na shekaru biyu da suka wuce
2017-03-04 14:01:20 cri
Yayin taron manema labarai da aka kira a yau Asabar dangane da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da za a fara a gobe Lahadi, kakakin taron, Madam Fu Ying ta bayyana cewa, kudin da aka kasafta a fannin tsaron kasar a shekarar 2017 zai karu da kimanin 7%.

Madam Fu Ying ta ce, "yawan kudin da muka kasfta a fannin tsaro ya kai kimanin kashi 1.3% na alkaluman ma'aunin tattalin arziki wato GDP, kuma ya kasance a wannan matsayi cikin shekaru."

Daga shekarar 2012 zuwa ta 2016, yawan kudin da kasar Sin ta kasfta ta fannin tsaro ya karu da kashi 11.2% da 10.7% da 12.2% da 10.1% da kuma 7.6% a jere, wato ke nan, yawan kasafin kudin tsaro na kasar Sin ya karu da kasa da kashi 10% cikin shekaru biyu a jere.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China