Firaministan kasar ta Nijar Brigi Rafini wanda a halin yanzu ya ke ziyara a kasar Aljeriya shi ne ya bayyana hakan. Yana mai cewa, kasashen biyu suna da kwarewa sosai a fagen yaki da ta'addanci.
Ya ce, manufar ziyarar tasa, ita ce musayar ra'ayoyi da jami'an Aljeriya a wasu muhimman batutuwa da suke shafar sassan biyu, ciki har da batun tsaro.
A jiya Laraba ne, Brigi Rafini ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Aljeriya bisa gayyatar takwaransa na Aljeriya Abdelmalek Sellal.
Wata sanarwa da ofishin firaministan na Nijar ya fitar tana cewa, ziyarar tasa wata dama ce da kasashen biyu za su yi amfani da ita wajen auna karfin dangantakar da ke tsakaninsu da kuma tsara hanyoyin kara zurfafa ta. (Ibrahim Yaya)