in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sace wani Baamurke kasar Nijar
2016-10-17 10:34:42 cri
A janhuriyar Nijar, ma'aikatar harkokin cikin gida, da tsaron jama'a, da ikon kananan hukumomi, da aikin addinai, ta sanar a ranar 15 ga wata cewa, wasu 'yan bindiga sun sace wani Baamurke a birnin Abalak dake jihar Tahoua a yammacin kasar.

A nasa bangare, gidan telabijin mallakar kasar, ya ba da labarin cewa, shugaban kasar Muhamadou Issoufou ya kira taron gaggawa na majalisar tsaron kasa a ranar Asabar, musamman domin tattauna hanyar da za a bi don warware wannan lamari. Daga bisani kuma, shugaban ya gana da jakadan kasar Amurka dake janhuriyar ta Nijar. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China