in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya da Tunisiya sun sake jaddada warware matsalar Libya ta hanyar siyasa
2017-03-06 10:46:46 cri
Jami'an kasashen Aljeriya da na Tunisiya, sun jaddada a jiya Lahadi cewa, ya zama dole a shawo kan matsalar kasar Libya ta hanyar siyasa.

Ministan kula da harkokin yankin Maghrib, da kungiyar tarayyar Afirka, gami da kawancen kasashen Larabawa na Aljeriya Abdelkader Messahel, ya yi shawarwari tare da ministan harkokin wajen Tunisiya Khemaies Jhinaoui, inda bangarorin biyu suka sake nanata cewa, ya kamata a himmatu wajen gudanar da shawarwari tsakanin bangarori masu ruwa da tsaki kan batun Liya, ta yadda za'a daidaita sabanin dake addabar kasa ta hanyar da ta dace.

Abdelkader Messahel ya kuma fadawa 'yan jaridu cewa, Aljeriya da Tunisiya dukkansu sun ki amincewa da duk wani katsalandan ta fuskar soja wanda sauran kasashe suke yi cikin batun Libya. Ya ce, ya fi kyau Majalisar Dinkin Duniya ta taka ta ta rawa a wannan batu. Mitsa Messahel ya bayyana cewa, kasarsa wato Aljeriya, na kara yin mu'amala da bangarori daban-daban na Libya, a wani kokari na daidaita matsalar ta hanyar gudanar da shawarwari. Haka kuma ya ce, Aljeriya za ta karbi bakuncin wani taro tsakanin kasashen dake makwabtaka da kasar ta Libya a farkon watan Afrilun bana.

Shi kuwa a nasa bangaren, ministan harkokin wajen Tunisiya, Khemaies Jhinaoui, na ganin cewa, bai kamata a yi amfani da karfin soji wajen warware matsalar Libya ba. Ya kuma ce shawarwari tsakanin shugabannin kasashe daban-daban a wannan yanki, za su taimaka matuka wajen warware wannan matsala. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China