Shafin intanet na TSA ya ba da labarin cewa, wani dan sanda ne ya budewa dan kunar bakin waken wuta a lokacin da ke kokarin tayar da bam din dake jikinsa a wajen ofishin 'yan sanda. Bayan dan kunar bakin waken ya fadi kasa ne kuma sai nan da nan ya tayar da bam din da ke makale a jikinsa, inda ya kashe kansa kana ya jikkata wasu jami'an 'yan sanda uku.
Sai dai jim kadan bayan kai wannan hari, mahukuntan kasar suka tura rukunin yaki da ayyukan ta'addanci zuwa wurin da lamarin da ya faru.
Kasar Aljeriya dai tana ci gaba da fuskantar barazanar ta'adddanci, sakamakon matsalar tsaro da rigingimun siyasa da yankin ke fuskanta. (Ibrahim)