in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude wani dandalin zabu jarin Afrika a birnin Alger
2016-12-04 12:56:57 cri
Dandalin zuba jari da harkokin kasuwanci ya bude kofa a ranar Asabar da yamma a karkashin jagorancin faraministan kasar Aljeriya Abdelmalek Sellal.

A wannan haduwa, kimanin shugabannin kamfanoni dubu biyu dake wakailtar kusan kasashen Afrika arba'in aka gayyata a wannan dandali.

Tare da matsalar faduwar farashin man fetur da ja da bayan kudin shiga na kasar, Aljeriya na fatan yawaita hanyoyin tattalin arzikinta ta hanyar kaddamar da ayyukan masana'antu da noma. Domin cimma wannan buri, gwamnatin kasar Aljeriya tana neman abokan hulda daga ketare.

A cikin jawabinsa na bude dandalin, faraministan Aljeriya ya nuna cewa Afrika na tabbatar da sunanta a dandalin kasa da kasa a matsayin wani yankin mai karfi da kuzari dake da muhimmanci sosai ta fannin siyasa da kuma tattalin arziki, da kuma maida hankali kan yaki da sabbin dalilai masu rauni. Amma duk da haka, ya nuna damuwa kan cewa musanyar tattalin arziki na tsakanin shiyya shiyya na wakiltar kawai kashi 12 cikin 100 a Afrika, a yayin da ya cimma kashi 40 cikin 100 a Amurka ta arewa da kuma kashi 60 cikin 100 a yammacin Turai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China