in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya za ta karbi taron G20 na 'yan kasuwa a karshen shekarar 2017
2016-12-05 10:08:13 cri
Kasar Aljeriya za ta karbi a shekarar 2017 da dandalin gungun G20 na 'yan kasuwa mai zuwa. Domin haka, an rattaba hannu kan wata yarjejeniyar shirya wannan muhimmin dandali a ranar Lahadi a birnin Alger tsakanin shugaban dandalin na shugabannin masu masana'antun Aljeriya (FCE) Ali Haddad da shugaban G20 na masana'antu, Gregoire Sentilhes. A yayin bikin sanya hannun da aka shirya a yayin dandalin Afrika kan zuba jari da harkokin kasuwanci, mista Sentilhes ya jaddada cewa wannan haduwa za ta gudana tsakanin karshen shekarar 2017 da farkon rabin shekarar 2018 domin nuna cewa 'yan Afrika su ne ginshikin bunkasuwa, makoma tana Afrika kuma mai yiyuwa za su kasance a tsakiyar juyin juya halin masana'antu na uku dake nan ke tasowa. A nasa bangare, mista Haddad ya bayyana cewa G20 na masana'antu, kamar yadda kuka sani, wata kungiyar duniya ce dake kunshe da manyan masana'antu fiye da 1500, muna farin cikin rattaba hannu kan wannan yarjejeniya kuma muna nan domin tarbon ku, in ji shi gaban bakonsa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China