in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya ta goyi bayan warware matsalar Libya ta hanyar yin shawarwari
2017-03-02 10:54:16 cri
Wani jami'in kasar Aljeriya ya jaddada a jiya Laraba cewar, Aljeriyar tana goyon bayan daidaita batun Libya ta hanyar gudanar da shawarwari.

Ministan kula da harkokin yankin Maghrib da kungiyar tarayyar Afirka gami da kawancen kasashen Larabawa na Aljeriya, Abdelkader Messahel, wanda ya bayyanawa 'yan jaridu hakan ya ce, kasarsa na ganin cewa, ya kamata al'ummar Libya su daidaita batun kasarsu ta hanyar yin shawarwari, kuma duk wata katsalandan daga wasu kasashe ba za ta magance batun yadda ya kamata ba. Abdelkader Messahel ya yi imanin cewa, jama'ar Libya za su iya daidaita matsalarsu da kansu.

Har wa yau kuma, Abdelkader Messahel ya sake nanata cewa, samun kwanciyar hankali mai dorewa a kasar ta Libya, na da alfanu sosai ga kasashen dake makwabtaka da ita, ciki har da Aljeriya, don haka, Aljeriya ta ki yarda da duk wani shisshigi daga kasashen waje, wanda ka iya haifar da illa ga kwanciyar hankali a wannan yanki.

A wani labari kuma, Abdelkader Messahel ya bayyana cewa, a karshen watan Maris na bana bangarorin masu ruwa da tsaki za su gudanar da taro game da batun Libya a kasar ta Aljeriya, a wani yunkuri na lalubo bakin zaren daidaita sabanin ra'ayi tsakanin bangarori daban-daban na kasar, ta yadda za'a samu kwanciyar hankali a kasar ta Libya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China