Tuni dai mahukuntan Aljeriya suka jibge dakarun tsaro har 10,000 a yankin dake kudancin iyakar kasa, a wani mataki na dakile kwararar mayakan kungiyoyin ta'addanci, da makamai daga wasu kasashe makwaftan ta.
A baya bayan nan dai an gano wurare da dama, wadanda mayakan sa kai ke boye makamai a kan iyakokin kasar da kasashen Mali, da Nijar da Libya, an kuma hallaka tare da kame 'yan ta'adda da dama yayin simame da sojin kasar ke kaddamarwa.
Kwararru ta fuskar tsaro na cewa, Aljeriya na yanki mai tattare da kalubalen tsaro, da yanayin siyasa maras tabbas, don haka dole ta dauki kwararan matakai, na dakile aukuwar hare hare daga 'yan ta'adda.(Saminu Alhassan)