Yau ne aka kaddamar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a birnin Beijing.
Yayin bikin kaddamarwar, firaministan gwamnatin kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da wani rahoto game da aikin da gwamnatin kasar Sin ta yi a shekarar ta 2016 da kuma wanda za ta yi a bana.
Wasu 'yan jarida na kasashen Afirka da ke daukar rahoton taron dake gudana a birnin Beijing, sun yabawa tarukan 2 na CPPCC da NPC.
Hordel Biakoro daga gidan telibijin na kasar Congo (Brazzaville) ya ce, gwamnatin Sin ta himmantu wajen kawo wa jama'arta ayyukan alkhairi, a kokarinta na inganta walwala da rayuwarsu. Kana Kataka daga kasar Togo ya yaba wa yadda ake gudanar da tarukan 2 yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)