in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara shekara na CPPCC
2017-03-03 15:33:22 cri

A yau Jumma'a da yamma agogon kasar Sin ne, aka bude taron shekara shekara na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC a nan birnin Beijing.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping gami da sauran shugabannin kasar sun halarci taron. Shugaban majalisar ta CPPCC, Mr. Yu Zhengsheng ya gabatar da rahoton aiki a wajen taron, inda aka waiwayi ayyukan da majalisar ta gudanar cikin shekarar da ta gabata, tare kuma da tsara ayyukan da za a gudanar a wannan shekara.

Majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ita ce ta ke tsara shawarwarin harkokin siyasar kasar da sa ido ta hanyar dimokuradiyya. Nan da kwanaki goma masu zuwa, 'yan majalisar sama da 2100 za su toba albarkacin bakinsu tare da ba da shawarwari kan muhimman batutuwan da suka shafi siyasa da tattalin arziki da matakan inganta rayuwar al'ummar Sinawa.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China