in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude taron shekara shekara na NPC a gobe da safe
2017-03-04 17:13:56 cri
Za a bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) da misalin karfe 9 na safiyar gobe Lahadi, agogon birnin Beijing.

A goben ne kuma za a saurari rahoton aikin gwamnati da firaministan kasar Li Keqiang zai gabatar, tare kuma da duba rahoton majalisar gudanarwar kasar, dangane da yadda aka aiwatar da shirin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma a shekarar 2016 da kuma daftarin shirin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma cikin shekarar 2017.

Har wa yau, za a duba rahoton majalisar gudanarwa, dangane da yadda aka aiwatar da shirin kasafin kudi a shekarar 2016 da kuma daftarin shirin kasafin kudi na shekarar 2017.

Da yammacin goben ne kuma, za a yi cikakken zama na 'yan majalisar, don yi nazari a kan rahoton aikin gwamnati.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China