Fu Ying wadda ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka kira yau Asabar da safe agogon birnin Beijing, ta ce yayin da taron ke gudana, za a kira tarurukan manema labarai har guda 17 a cibiyar watsa labarai.
Madam Fu Ying ta ce, ban da rahoton aikin gwamnati da ma sauran wasu rahotanni da za a duba kamar yadda aka saba a yayin taron, za kuma a yi nazari kan wasu batutuwa 11, da suka hada da nazarin daftarin ka'idojin dokokin kare al'umma da ma wasu shirye-shirye uku da suka shafi zabar sabbin 'yan majalisar karo na 12.
Madam Fu Ying ta kara da cewa, za a rufe taron ne a ranar 15 ga wata da safe, kuma a lokacin ne firaministan kasar, Li Keqiang zai gana da manema labarai na gida da waje.
Har ila yau, ta ce za a bada damar kasancewa a zauren taron ga 'yan jarida na gida da na waje, baya ga damar da za su samu ta tattaunawa da 'yan majalisar.
Bugu da kari, daga cikin tarukan manema labarai 17 da za a shirya, a ranar 6 ga wata, shugaban kwamitin kula da harkokin ci gaba da gyare-gyare na kasar zai gana da manema labarai, sai kuma ministan kudi da ministan harkokin waje da ministan kiyaye muhalli da ma ministan kasuwanci wadanda za su gana da 'yan jaridar a ranakun 6 zuwa 9 da kuma ranar 11 ga wata.
Kakakin ta kara da cewa, kawo yanzu, 'yan jarida sama da 3,000 ne suka yi rajista domin dauka rahoton taron, kuma rabi daga cikinsu sun fito ne daga wasu kasashe 9. (Lubabatu)