Shugaban kwamitin John Chilcot wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce daukar matakin soja ba shi ne matakin karshe da ya dace a dauka a yakin na Iraki ba.
Bugu da kari, kwamitin binciken ya gano cewa,firaministan Burtaniya na wancan lokaci Tony Blair ya shaidawa tsohon shugaban Amurka George Bush watanni da dama kafin su kaddamar da shirin mamaye kasar Iraki cewa,yana tare da shi a kowane hali dangane da kasar ta Iraki. (Ibrahim)