Rahotanni na nuna cewa, sojojin kasar Sin sun shafe shekaru 14 suna aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Liberia, wato tun daga shekarar 2003.
A lokacin da sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin suke gudanar da ayyukansu a kasar Liberia, sun yi nasarar binciken da MDD ta yi musu kan kayayyakin da suka yi amfani da su da kuma kwarewarsu wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya. Sojojin sun yi aiki da motoci kimanin dubu 8, sun kuma gudanar da bincike da gyara hanyoyi sama da kilomita 500, da gina da kuma gyara gadoji fiye da guda 10. Haka kuma, sun yi jigilar kayayyakin agaji sama da ton dubu 6, baya ga gudanar da ayyukan ceto sanadiyar tashin gobara, da samar da kayayyakin taimako, gyara gidaje, da kuma yin aikin sintiri da dai sauransu.
Wannan ya sa, MDD ta karrama dukkan sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin da lambar yabo saboda ayyukan da suka gudanar. (Maryam)