Shirin na kwanaki 10 wanda ma'aikatar tsaro kasar Sin tare da hadin gwiwar MDD ke daukar nauyinsa,zai mayar da hankali ne wajen koyar da matan dabarun aikin kiyaye zaman lafiya da ayyukan jin kai, kare mata ta kananan yara da kuma amfani da karfi idan bukatar hakan ta taso.
A shekarar 2015 ne kasaar Sin ta yi alkawarin horas da ma'aikatan kiyaye zaman lafiya 2,000 daga ko'ina a duniya na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Bayanai na nuna cewa,ya zuwa yanzu sama da masu kayan sarki daga kasar Sin 30,000 ne suke aikin kiyaye zaman lafiya a wurare 24. Sannan an kashe dakarun kasar 11 a lokacin da suke bakin aiki.
Kimanin sojoji mata 40 ne za su halarci kwas din da ke gudana a halin yanzu.(Ibrahim)