in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zargin da kungiya mai zaman kanta ta Amurka ta yiwa sojojin Sin dake Sudan ta Kudu ba gaskiya ba ne, in ji ma'aikatar tsaron Sin
2016-10-11 10:53:46 cri

An ba da labari cewa, wata kungiya mai zaman kanta mai suna "fararen hula dake fama da rikici" dake birnin Washington na kasar Amurka ta ba da wani rahoto kan rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD ta daidaita rikicin da ya faru a birnin Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu a watan Yuli, inda aka zargi ayyukan da rundunar kiyaye zaman lafiya ta Sin dake kasar. A game da haka, kakakin ma'aikatar tsaro ta Sin Yang Yujun ya bayyana a yau Talata cewa, wannan zargi bai dace da hakikanin hali ba.

"A watan Yulin wannan shekara, rikici ya kaure a Sudan ta Kudu, bisa umurnin da ofishin hafsan-hafsoshin tawagar MDD dake kasar Sudan ta Kudu ya bayar, rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta Sin dake kasar ta dauki nauyin kiyaye tsaron sansanin 'yan gudun hijira mai lamba 1 dake dab da hedkwatar tawagar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD a birnin Juba, domin kare rayukan jami'an kiyaye zaman lafiya da kuma 'yan gudun hijira. A ranar 10 ga watan Yuli, rikicin ya kara tsananta, sojojin Sin sun nace ga guraben ayyukansu, wata motarsu ta fuskanci harin boma-bomai, a sakamakon haka, sojojin Sin Li Lei da Yang Shupeng sun rasa rayukansu, kana wasu sojoji 5 sun jikkata."

Duk da cewar, wadannan sojojin Sin sun mutu, wasu kuma sun jikkata, amma rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta Sin ta ci gaba da sauke nauyin dake bisa wuyanta. Mr. Yang Yujun ya kara da cewa, kafin MDD ta sanar da rahoton bincike, kowane irin zargin da aka yi wa sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD ba shi da sahihanci.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China