Kwamitin sulhu na MDD ya yi muhawara a jiya Jumma'a, domin tattauna kan ayyukan kare rayukan fararen hula a yayin da ake gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya, tare da yadda za a inganta hadin gwiwa da kasashen dake fama da rikici da kuma kungiyoyin kasa da kasa ta hanyar kyautata aikin ba da izni na kwamitin sulhu na MDD domin inganta aikin kiyaye zaman lafiya.
Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya bayyana a gun taron cewa, kare rayukan fararen hula ya fi muhimmanci daga cikin dukkan ayyukan MDD. Dole ne a ba da izni da daukar matakan siyasa masu daidaici wajen kare rayukan fararen hula a lokacin ayyukan kiyaye zaman lafiya.
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana cewa, ya kamata kasashen da suka tura sojojin kiyaye zaman lafiya su kara karfin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya, domin tabbatar da ingancin makamashi da makamai da kungiyoyin kiyaye zaman lafiya za su samu. Ya kuma jaddada cewa, daidaita muhimman batutuwa ta hanyar siyasa ita ce hanya mafi kyau wajen kare rayukan fararen hula.
Zaunanniyar wakiliyar kasar Amurka dake MDD Samantha Power ta yi jawabi cewa, sojojin kiyaye zaman lafiya su kan fuskanci hadura sosai a yayin da suke gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya. A kwanan baya, wasu sojojin kiyaye zaman lafiya da suka fito daga kasashen Togo da Sin da Habasha da sauransu sun mutu ko jikkata a sakamakon hare-hare. A madadin gwamnati da jama'ar kasar Amurka, ta jajanta wa iyalan wadannan mutanen da suka mutu ko jikkata da ma kasashensu, tare da nuna godiya ga gundummowar da suka bayar.(Lami)