in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta cika alkawarinta a fannin ayyukan kiyaye zaman lafiya, in ji mataimakin babban magatakardan MDD
2016-09-09 09:37:11 cri

Mataimakin babban magatakardan MDD mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya Herve Ladsous ya bayyana a gun taron manema labaru na MDD da aka yi a jiya Alhamis a birnin London cewa, kudurin da kasar Sin ta dauka wajen goyon bayan ayyukan kiyaye zaman lafiya na da muhimmanci sosai, Sin ta cika alkawarinta game da wannan aiki.

Herve Ladsous ya bayyana cewa, kasar Sin ta sanar a gun wannan taro cewa, za ta goyi bayan shawarar da MDD ta dauka wajen jibge sojojin kiyaye zaman lafiya cikin gaggawa. Ya kuma kara da cewa, kasar Sin kasa ce da ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya mafi yawa daga cikin zaunannan kasashen kwamitin sulhu na MDD. An tura sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin a wurare daban daban masu hadarin gaske, wasu daga cikinsu sun mutu a kwanan baya, kasar Sin ta cika alkawarinta da kuma nuna niyyarta wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a duniya.

A wannan rana kuma, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ba da sanarwa cewa, yana maraba da kasashe daban daban da su cika alkawari a gun taron ministoci kan harkokin kiyaye zaman lafiya na MDD da aka yi a birnin London, domin jibge sojojin kiyaye zaman lafiya cikin gaggawa. Ban Ki-moon ya nanata cewa, MDD za ta dukufa kan kyautata ayyukan kiyaye zaman lafiya tare da kasashen da suka tura sojojin kiyaye zaman lafiya, ciki har da yaki da cin zarafin mata da kuma yi musu fyade. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China