Yau Laraba rana ce ta wanzar da zaman lafiya a duniya. Gabanin wannan rana a 'yan kwanakin da suka gabata, babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya gabatar da wani jawabi game da ranar, inda a cikin sa ya yi kira da a tabbatar da burin samun dawamammen ci gaba, domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a duniya baki daya.
Ban Ki-Moon ya kuma bayyana cewa, a ranar wanzar da zaman lafiya ta duniya ta kowace shekara, MDD kan yi kira ga bangarori daban daban dake dauki ba dadi da suka ajiye makaman su, su tsagaita bude wuta har tsawon sa'o'i 24.
Babban magatakardan MDDr ya ce a ranar wanzar da zaman lafiya ta wannan shekara, an jaddada bururruka 17 na neman samun dawamammen ci gaba, wadanda suka samar da wani tushe na kiyaye zaman lafiya. Kaza lika ya ce, a watan Satumbar shekarar bara, kasashe mambobin MDD 193, sun zartas da kudurin neman samun dawamammen ci gaba, matakin da ke da matukar muhimmanci wajen kiyaye zaman lafiya. (Lami)