Kumbon 'Chang-e' mai lamba hudu zai kaddamar da mataki na hudu na aikin binciken duniyar wata na kasar Sin
Babban mai jagora, kana babban mashawarci kan tsara fasalin taurarin dan Adam dake binciken duniyar wata na kamfanin kula da kimiyya da fasahar sararin samaniya na kasar Sin, Mista Ye Peijian ya bayyana yau cewa, kasar Sin za ta kaddamar da mataki na hudu na katafaren aikin binciken duniyar wata nan bada jimawa ba.
Mista Ye ya yi karin haske da cewa, a wannan mataki, kasar Sin za ta aika na'urorinta na bincike zuwa karin wuraren dake duniyar wata, kuma za'a kara tura na'urorin mutum-mutumi don su shiga cikin ayyukan gudanar da bincike.
Za dai a harba kumbo mai suna 'Chang-e' mai lamba hudu a badi.(Murtala Zhang)