in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kumbon Tiangong-2 yana kokarin hadewa da wani kumbon da aka harba
2016-09-26 10:15:16 cri

A jiya ne masana kimiyya na kasar Sin suka karkata kumbon binciken Tiangong mai lamba 2 zuwa dai-dai nisan kilomita 393 daga doron duniya, a kokarin da ake na hade kumbon da takwaransa na Shenzhou-11 wanda ake shirin harba shi a cikin wata mai zuwa.

Mataimakin shugaban cibiyar kula da harba tauraron dan-Adan ta kasar Sin Li Jian, ya ce tuni dai kumbom Tiangong-2 wanda aka harba shi daga cibiyar harba tauraron dan-Adam ta Jiuquan a ranar 15 ga watan Satumba, ya shiga kwanaki na 9 na gwaje-gwajen da ya ke gudanarwa a sararin samaniya, kafin a karkata shi a jiya.

Ana sa ran za a harba 'yan sama jannati guda 2 a cikin kumbon na Shenzhou-11 domin hadewa da kumbon na Tiangong-2 a cikin watan Oktoba. Kuma 'yan sama jannatin za su yi aiki ne a dakin bincken kunbon na tsawon kwanaki 30 kafin su dawo doron duniya.

Li ya ce, hadewar kumbunan biyu, ita ce fasahar hade kumbuna na farko da kasar Sin za ta gudanar a tashar binciken sararin samaniya da ta ke fatan ginawa a nan gaba, inda kumbon da 'yan sama jannatin ke sarrafa shi ya ke kokarin hadewa a tashar bincken sararin samaniya ta hanyar amfani da fasahohinta na binciken sararin samaniya.

A watan Afrilun shekarar 2017 ne kasar Sin za ta harba kumbon dakon kaya na Tianzhou-1 zuwa sararin samaniya, inda zai hade da dakin binciken sararin samaniya, a wani mataki na samar da mai da sauran muhimman kayayyakin da ake bukata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China