in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sama jannati daga Shenzhou-11 sun shiga dakin bincike na Tiangong-2
2016-10-19 08:59:03 cri

Yan sama jannatin kasar Sin Jing Haipeng, da Chen Dong sun shiga dakin bincike na Tiangong-2, da misalin karfe 6:32 na safiyar jiya Laraba, bayan da kunbon Shenzhou-11 ya yi jigilar su daga tashar harba kumbuna ta Gobi a ranar Litinin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, 'yan sama jannatin za su kasance a tashar binciken samaniya tsawon kwanaki 30 kafin su dawo doron duniya. Kunbon Shenzhou-11 ya hadu da cibiyar bincike ta Tiangong-2 da misalin karfe 3:31 na asubahin ranar Laraba.

Kasar Sin ce dai kasa ta uku baya ga Rasha da Amurka, a jerin kasashen duniya da suka samu cikakkiyar nasarar harba kunbunan bincike zuwa sararin samaniya.

Tun a ranar 15 ga watan Satumbar da ya gabata ne dai kasar Sin ta harba kumbon bincike na Tiangong-2, kumbon da ya zamo muhimmin mataki, a yunkurin da kasar ke yi na kafa tashar sararin samaniya ta din din din nan da shekara ta 2020.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China