in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a harba kumbon Shenzhou-11 a gobe Litinin da karfe 7 da rabi na safe
2016-10-16 12:59:57 cri

Za a harba kumbon Shenzhou-11 mai dauke da mutane a gobe Litinin da karfe 7 da rabi na safe, tare da 'yan sama jannati biyu, Jing Haipeng da Chen Dong.

Mataimakiyar darektan ofishin kula da kumbo mai dauke da mutane a sararin samaniya na kasar Sin Wu Ping ta gabatar da wannan labari a cibiyar harba tauraron dan Adam dake birnin Jiuquan na Sin.

Madam Wu Ping ta kuma kara da cewa, Jing Haipeng shi zai zama mai ba da umurni a cikin wannan kaumbo, Mr. Jing ya taba zuwa sararrin samaniya a cikin kumbon Shenzhou-7 da kumbon Shenzhou-9, amma Mr. Chen Dong zai yi wannan aiki karo na farko.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China