Da safiyar yau din nan ne Sin ta harba kumbo mai dauke da mutane samfurin Shenzhou 11 cikin nasara, inda nan take Xi Jinping, babban sakataren jam'iyyar JKS, kuma shugaban kasar Sin kana shugaban kwamitin aikin soji na kasar Sin wanda ke halartar ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 8 a Goa na kasar Indiya ya aike da sakon taya murnar wannan aiki.
Da karfe 7 da rabi da safiyar yau Litinin ne dai aka harba kumbo mai dauke da mutane samfurin Shenzhou 11 cikin nasara, aikin da ya zamo mai muhimmanci wajen samar da kayayyaki ga 'yan sama jannati dake aiki a tashar gwajin sararin sama samfurin Tiangong 2, tare kuma da yin gwajin fasahar hada kumbon da tashar gwajin sararin sama, da fasahar sauko da kumbo daga sararin sama, kana ana sa ran za a hada kumbon da Tiangong 2 domin samar da wurin zama ga 'yan sama jannati, ban da haka kuma ana fatan za a gudanar da gwajin fasahohin da mutane suke yi da kansu a sararin sama kamar su gwajin likitanci da gwajin kimiyya da gyara ga kumbon da dai sauransu.(Jamila)