in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta harba kumbo mai dauke da mutane samfurin Shenzhou 11 cikin nasara
2016-10-17 08:00:42 cri

Yau Litinin 17 ga wata da misalin karfe 7 da rabi da safe, an harba kumbo mai dauke da mutane samfurin Shenzhou 11 cikin nasara a nan kasar Sin, muhimmin aikin kumbon shi ne samar da kayayyaki ga 'yan sama jannati dake aiki a tashar gwajin sararin sama samfurin Tiangong 2, tare kuma da yin gwajin fasahar hada kumbon da tashar gwajin sararin sama da fasahar sauko da kumbo daga sararin sama, kana ana sa ran za a hada kumbon da Tiangong 2 domin samar da wurin zama ga 'yan sama jannati, ban da haka kuma ana fatan za a gudanar da gwajin fasahohin da mutane suke yi da kansu a sararin sama kamar su gwajin likitanci da gwajin kimiyya da gyara ga kumbon da dai sauransu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China