Ya zuwa yanzu, kumbon mai dauke da 'yan sama jannati guda biyu, watau Jing Haipeng da Chen Dong, ya yi kewaye kan wata da'ira a tsawon kwanaki 33. Kuma bisa shirin da aka tsara, kumbon Shenzhou 11 ya bari tashar gwajin sararin sama ta kumbon Tiangong 2 a jiya Alhamis, sa'an nan zai iso doron duniya a yau Juma'a da yamma. (Maryam)