Mr.Guterres ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 34 da aka bude a wannan rana, haka zalika ya ce, ya kamata kasashen duniya su nuna adalci game da batutuwan da suka shafi harkokin kare hakkin dan Adam, sabo da ta wannan hanya ce kawai za a karfafa hadin gwiwar kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD ta yadda zai samu amincewa daga al'ummar duniya. (Maryam)