Cikin jawabinsa, Fu Cong ya ce kiwon lafiya shi ne tushen kare hakkin dan Adam, yana kuma taimakawa wajen cimma burin kiyaye sauran hakkokin dan Adam. Ya ce al'ummar duniya na da bukatar samun kulawa mai kyau ta fuskar kiwon lafiya, domin jin dadin zaman rayuwa cikin mutunci. Sai dai a hannu guda an sha fama da yaduwar cututtuka da dama a sassan duniya, kamar su cutar kanjamau, da Ebola, da zazzabin cizon sauro da dai sauransu. Ban da wannan kuma, akwai bukatar a yi kokari don rage adadin rasuwa, da rashin lafiyar yara kanana.
Fu ya kara da cewa, akwai bambanci a tsakanin kasashen duniya game da gudanar da ayyukan kiwon lafiyar jama'a. Ya zama dole a inganta harkokin kiwon lafiya, da gina ababen more rayuwa na kasa da kasa, domin kawar da rashin daidaito a tsakanin kasashe daban daban a fannonin samun hidima, da labarai, da ilmi a wannan fanni, musamman ma kamata ya yi a kara kokarin kawar da bambancin da ake nuna wa mutane masu karamin karfi. (Maryam)