Ma Zhaoxu ya ce, aikin kare hakkin bil Adama shi ne aikin kasa da kasa, shi ya sa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su yi hadin gwiwa domin kyautata wannan aiki, a da ake murnar cikon shekaru 10 da kafa kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, ya kamata a yi amfani da ilmi da darusa da aka samu kan batun cikin wadannan shekarun da suka gabata wajen taimaka wa kwamitin domin ciyar da ayyukansa gaba.
Ban da haka kuma, mista Ma ya bayyana cewa, ana fatan MDD za ta iya nuna wa kasar Sin adalci wajen binciken yanayin hakkin dan Adam na kasar da kuma daga dukkan fannoni, domin ba da taimako ga kasar Sin wajen kara kyautata wannan aiki yadda ya kamata, a maimakon janyo mata matsalolin da basu kamata ba.
Bugu da kari, ya ce, ko da yake, kasar Sin ta riga ta yi cikakken bayani na musamman kan harkar da wasu dokokin kasar da abin ya shafa ga ofishin babban kwamishinan MDD dake kula da harkokin hakkin dan Adam, amma kwamishinan ya yi ta fidda munanan bayanan da bai kamata ba kan yanayin kasar Sin, lamarin da ya bata wa kasar rai sosai. Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen gudanar da harkokin kasar bisa dokoki, kuma ta tsara dokokinta bisa babbar manufar kiyaye iko da 'yanci na al'ummominta, har ma da na kungiyoyi masu zaman kansu na ketare baki daya, haka kuma, cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa kan kyautata ayyukan kare hakkin dan Adam. (Maryam)