Cikin sanarwar, Zeid Ra'ad Al Hussein ya ce, mutane a kasar Amurka ko da suka taba zaman kurkuku, shan miyagun kwayoyi, akwai matsalar tabuwan hankali da kuma yin mu'amala da masu tsattsauran ra'ayi na kasar da na waje, za su iya sayan bindigogi iri daban daban, lamarin da ya taba mana rai kware da gaske.
Haka kuma, ya ce, ganin hare-haren bindigogin da suka taba aukuwa a wasu wuraren kasa da kasa, ya kamata a kafa dokokin da suke dace a hana saya da yin amfani da bindigogi, amma a kasar Amurka, akwai bindigogi masu dimbin yawa dake hanayen al'ummomin kasar, lamarin da ya haddasa rasuwa ko jikkatar dubban mutane a kasar cikin ko wace shekara. (Maryam)