Cikin jawabi nasa, Mr. Ma ya ba da shawarwari guda bakwai da suka hada da cewa, ya kamata kasa da kasa su bi manufofi da ka'idojin kundin MDD yadda ya kamata, domin ba da taimako wajen cimma muradun neman dauwamammen ci gaba na shekarar 2030, domin samar da harsashi na kiyaye hakkin dan Adam da kuma ciyar da harkokin hakkin dan Adam gaba, sa'an nan, ya kamata a neman ci gaba yayin da ake mai da hankali kan kyautata zaman rayuwar al'ummomin duniya, yayin da ake kuma kiyaye da raya hakkin dan Adam daga dukkan fannoni, kamar raya ikonsu na neman ci gaba, haka zalika, ya kamata a neman ci gaban hakkin dan Adam cikin daidaituwa, domin inganta yanayin adalci na zaman takewar al'umma, sa'an nan kuma, ya kamata a tsaya tsayin daka wajen neman ci gaba ta hanyoyi daban daban, domin samar da karin manufofi kan ayyukan kiyaye hakkin dan Adam da kuma ciyar da hakkin dan Adam gaba, bugu da kari, ya kamata a yi shawarwari da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, yayin da ake ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen gina da kuma karfafa ayyukansu na kiyaye hakkin dan Adam, daga bisani kuma, ya kamata a kiyaye ka'idoji na nuna fahimtar juna da adalci, da yin koyi da juna, da kuma yin hadin gwiwa domin cimma moriyar juna, ta yadda za a iya ciyar da bunkasuwar kasa da kasa gaba, yayin da ake cimma burinmu na kiyaye hakkin dan Adam yadda ya kamata a nan duniya, a karshe dai, ya kamata a mai da hankali kan harkokin kiyaye hakkin dan Adam ko da yaushe a yayin da muke neman ci gaba. (Maryam)