Kwamiti na 3 mai kula da harkokin zamantakewar al'umma, jin kai da al'adu na babban taron MDD karo na 70 ya yi muhawara kan batun hakkin dan Adam a wannan rana, inda Liu Jieyi ya yi jawabi cewa, kamata ya yi kasa da kasa su girmama hanyoyi iri daban daban wajen tabbatar da hakkin dan Adam, da duba yanayin hakkin dan Adam cikin adalci, da yin hadin gwiwa da warware matsaloli ta hanyar yin shawarwari, da kuma neman hanya mai dacewa wajen sa kaimi ga tabbatar da hakkin dan Adam.
Hakazalika kuma, Liu Jieyi ya bayyana cewa, kasar Sin tana bin ra'ayin yin imani da juna, amincewa da bambance-bambance, hadin gwiwa da samun moriyar juna, da kuma tana goyon baya da shiga ayyukan raya sha'anin tabbatar da hakkin dan Adam na duniya. Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci tarurukan tunawa da cika shekaru 70 da kafuwar MDD, ya sanar da wasu manyan manufofi, wadanda suka shaida cewa, kasar Sin kasa ce da ta sa kaimi da bada gudummawa wajen raya sha'anin tabbatar da hakkin dan Adam na duniya. (Zainab)