Mr. Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, bangaren Sin ba zai amince da yadda wasu kasashe ke amfani da batun kare hakkin dan Adama a matsayin siyasa ba. A waje daya, ya jaddada cewa, babu wata hanya tak a duniya da ake amfani da ita wajen kiyaye hakkin dan Adama. A saboda haka, dole ne kowace kasa ta kiyaye harkokin da suka shafi kare hakkin dan Adama bisa hakikanin halin da kasar take ciki ta yadda zai dace da bukatun al'ummarta.
Ran 10 ga wata Disamba rana ce ta kare hakkin Adama ta duniya karo na 68. (Sanusi Chen)