Rahoton ya kuma bayyana cewa, tun daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2015, kasar Sin ta dukufa wajen tabbatar da ikon al'ummomin kasar kan tattalin arziki, zaman takewar al'umma da kuma al'adu, inda ta kuma kyautata tsarin gudanarwar ayyukan kasa bisa fasahohin zamani domin kare ikon siyasar jama'ar kasar yadda ya kamta, haka zalika, kasar ta ciyar da nazari kan ilmin hakkin dan Adam da koyar da ilmin a kasar gaba, domin kara sanin jama'ar kasa kan harkokin da abin ya shafa da kuma yin shawarwari kan batun bisa ka'idojin nuna adalci da mutuntawa.
Bugu da kari, kasar ta aiwatar da yarjejeniyoyin kasa da kasa da abin ya shafa yadda ya kamata cikin shekarun baya bayan nan, inda ta kuma ba da gudummawa wajen raya aikin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa.
Don haka, a karshen shekarar 2015, kasar Sin ta kammala shirinta na kyautata yanayin kare hakkin dan Adam na shekarar 2012 zuwa shekarar 2015 cikin yanayi mai kyau da kuma bisa dukkan fannoni. (Maryam)