Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, kasar Sin za ta yi amfani da damar zama mamban kwamitin kula da kare hakkin dan Adam wajen kara ba da babbar gudummowa a fannin kiyaye hakkin dan Adam a duniya.
A ranar 28 ga wata ne babban taron MDD karo na 71 ya jefa kuri'ar zaben mambobin kwamitin harkokin kare hakkin dan Adam na shekarar 2017 zuwa shekarar 2019, inda kasar Sin ta samu kuri'u 180, wanda ya ba ta damar zama mamban kwamitin a karo na 4 tun bayan kafuwar kwamitin. (Tasallah Yuan)