in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun raguwar cinikin namun daji ba bisa doka ba a Sin
2017-02-27 13:04:27 cri
Hukumar kula da gandun daji ta kasar Sin ta bayyana a jiya Lahadi cewa, har yanzu ana samun masu sarautar namun daji da tsire-tsire, amma daga shekarar da ta gabata, ya zuwa yanzu, adadin cinikin namun daji da tsire-tsire yana ci gaba da raguwa a nan kasar Sin.

Mataimakin shugaban hukumar kula da gandun daji ta kasar Sin Liu Dongsheng ya bayyana cewa, adadin fasa kwaurin hauren giwa da aka kama ya ragu da kashi 80 bisa dari idan aka kwatanta da adadin shekarar da aka mafi samun fasa kwaurin hauren giwa, haka kuma, kasar Sin za ta dakatar da ciniki da amfani da hauren giwa a karshen shekarar bana, a wani mataki na taimakawa kasashen Afirka kare giwayen dake nahiyar, ta yadda za a rage bukatun kayayyakin hauren giwa a kasar.

Mr. Liu ya bayyana haka ne a yayin bikin bude shirye-shiryen ranar namun daji da tsire-tsire na kasa da kasa karo na hudu da aka yi a gidan dabbobi dake birnin Beijing.

Tun ranar 1 ga watan Janairu na shekarar bana ne, aka fara amfani da sabuwar dokar kiyaye namun daji a kasar Sin domin kiyaye namun daji yadda ya kamata, inda aka karfafa horon da aka yi wa masu laifin safara da cin namun daji da kuma masu aikata cinikin namun daji. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China