in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Zuma ya kaddamar da cibiyar yaki da karkanda
2015-11-02 10:32:01 cri
A jiya Lahadi ne shugaba Jacob Zuma na kasar Afirka ta kudu ya kaddamar da wata cibiyar yaki da karkanda a gandun dajin Kruger a kokarin kawo karshen yadda ake ci gaba da farautar dabbar ta karkanda a kasar.

A jawabin da ya gabatar yayin kaddamar da cibiyar, shugaba Zuma ya jaddada muhimmancin rawar da al'umma za ta taka wajen kare namun daji baki daya. Ya bayyana cewa, idan har al'umma ta tashi tsaye wajen kare dabbar karkanda, hakan zai taimaka wajen kare daukacin al'umma daga fadawa kangin talauci, karuwar munanan ayyuka har ma da fadawa cikin kuncin rayuwa.

A shekarar 2011 ne gwamnatin Afirka ta kudu ta kara tsaurara matakan da take dauka kan hana farautar karkanda, tun lokacin da kasar ta ayyana farautar karkanda a matsayin barazanar tsaro ga kasa. Matakin da ya samu amincewar majalisar zartaswar kasar a shekarar 2014.

Bugu da kari, kasar ta Afirka ta kudu ta kara cimma yarjejeniya da kasashen Vietnam, Sin, Cambodia da kuma Mozambique a wani mataki na kawo karshen farauta da kuma cinikin namun daji ba bisa ka'ida ba a duniya baki daya.

Ana fatan ayyukan cibiyar za su taimaka a yakin da ake da karkanda da ma ragowar namun daji da ke dab da bacewa a doron kasa. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China