in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen tsakiyar Afrika na neman hanyoyin yaki da manyan laifuffuka
2015-09-01 11:18:25 cri

Wakilai na kasashen dake tsakiyar Afrika, dake samun goyon bayan ofishin yaki da miyagun kwayoyi da manyan laifuffuka na MDD UNODC, na taro a birnin Brazzaville na kasar Congo, tun daga ranar 31 ga watan Augusta zuwa 3 ga watan Satumba domin yin nazari kan hanyoyin karfafa sanya ido kan iyakokinsu domin yaki da laifuffuka game da namun daji.

A karkashin jagorancin kungiyar tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika, da hukumar dake kula da dazuzzukan kasashen tsakiyar Afrika, tare da tallafin UNODC, wannan dandali ya kasance na farko da ake shiryawa kan matakan karfafa sanya ido kan iyakoki na shirin aiwatar da tsarin duniya na yaki da manyan laifuffukan dake da nasaba namun daji.

Manufar ita ce don karfafa matakai a bangaren cikin gida da kuma kasa da kasa, yin aiki tare tsakanin hukumomin daban daban dake kula da yaki da safara da kasuwancin kayayyaki da namun daji, da na dazuzzuka ba bisa doka ba.

A cewar kwararru, farautar namun daji na daukar wani sabon salo dake karuwa a tsakiyar Afrika, inda kungiyoyi masu aikata mayan laifuffuka suke yin amfani da makamai da harsasai na yaki, motoci da wasu hanyoyin sadarwa na zamani.

A cewar ministan tattalin arzikin dazuzzuka da ci gaba mai karko na Congo, Henri Djombo, wannan annoba ta janyo hasarar fiye da kashi 60 cikin 100 na giwaye a Congo a tsawon shekaru goma na baya bayan nan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China