in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da sarkin Kano
2017-02-27 10:53:03 cri

A daren ranar 25 ga wata, bisa gayyatar da jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian ya yi masa, tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, kana sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu ya kai ziyara ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Nijeriya.

A yayin ganawar tasu, malam Sanusi ya bayyana cewa, jihar Kano ita ce cibiyar jima, saka da kuma rini a arewacin Nijeriya, saboda haka tana fatan kamfanonin kasar Sin za su gaggauta zuba jari a jihar, ta yadda za a raya sana'ar kera kayayyaki, tare da samar da karin guraben ayyukan yi a jihar.

A nasa bangare, Zhou Pingjian ya ce, kasar Sin tana son yin musayar fasahohi a tsakaninta da kasar Nijeriya kan yadda za a bunkasa sana'ar kera kayyayaki, amma kamfanonin kasar Sin za su yanke shawarar ce bisa la'akari da harkokin kasuwanci da abin ya shafa kan ko za su zuba jari a kasar Nijeriya ko a'a. A don haka bai kamata gwamnatin kasar Sin ta tsoma baki kan wannan batun ba. Haka kuma, yana ganin cewa, idan yankin arewancin Nijeriya yana son kamfanonin kasar Sin su kara zuba jari a yankin, to ya kamata yankin ya kara bude kofarsa ga kasashen waje, kana ya kara bullo da karin manufofin hidima ga kamfanonin waje wadanda suke son zuba jari a yankin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China