in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin a Najeriya ya shirya bikin nuna fina-finai game da harkokin Tibet
2016-04-28 10:38:36 cri

 

Jiya Laraba 27 ga wata, ofishin jakadancin kasar Sin dake tarayyar Najeriya ya shirya bikin nuna fina-finan dake shafar harkokin yankin Tibet na kasar Sin, bikin da ya samu halartar wakilan ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, da jami'an ma'aikatar watsa labaran kasar, da 'yan jaridun manyan kafofin watsa labarai. Sauran wadanda suka halarci bikin sun kunshi manyan masana a hukumar nazari da ba da shawara, da wakilan kungiyoyin nazari, da wakilan kungiyoyi masu zaman kan su sama da dari.

A yayin da yake jawabi wajen bikin, jakadan kasar Sin dake Najeriya Gu Xiaojie, ya bayyana cewa shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 45 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da Najeriya, kana, cikin wadannan shekaru 45 da suka wuce, an yi ta bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin kyakkyawan yanayi, yayin da cimma sakamako da dama, bisa hadin gwiwar kasashen biyu.

Kaza lika, malam Gu ya ce, ya kamata kasashen biyu su ci gaba da karfafa mu'amalar su, yayin da suke dukufa wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka amince a fannin hadin gwiwa yadda ya kamata.

Daga bisani kuma, a nasa tsokaci kan bunkasuwar yankin Tibet mai cin gashin kan sa na kasar Sin, malam Gu ya nuna cewa, sakamakon tsarin musamman na yankin mai cin gashin kansa, yankin Tibet ya samu ci gaba matuka cikin shekarun da suka gabata, inda GDPn yankin ya ninka sau 313 a shekarar 2015, idan aka kwatanta da na shekarar 1965.

Bugu da kari, a yayin bikin, an nuna fim mai taken "samaniyar yankin Tibet", wanda ya nuna bunkasuwar yankin, haka kuma, masu kallo daga Najeriya sun bayyana cewa, bikin na da matukar ma'ana, ya kuma ba su sha'awa, inda ta ba su damar zurfafa fahimtar su game da yankin Tibet, da ma al'adun kasar Sin, wanda hakan ya kara musu imani kan bunkasuwar dangantaka tsakanin kasashen Sin da Najeriya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China