Olagunju ya yi nuni a cikin jawabinsa mai taken "dangantakar dake tsakanin Nijeriya da Sin: abubuwan da ke taimakawa bunkasuwar kasa" cewa, yayin da shugaban kasar Nijeriya Buhari ya kawo ziyara kasar Sin, bankin masana'antu ya tura wata tawagar manyan jami'an bankinsa da suka tafe tare da shugaba Buhari, ta yadda za a inganta hadin gwiwa a tsakanin bankunan Nijeriya da Sin.
Game da matakan raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Nijeriya da Sin kuwa, Olagunju ya yi nuni da cewa, akwai bukatar a daga darajar kayayyakin da kasar Nijeriya take kerawa don warware matsalar rashin daidaiton cinikayya a tsakanin kasashen biyu. Kana ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kaunaci kasarsu, maimakon zargi wasu kasashe da hannu a mawuyacin halin da fannin tattalin arzikin kasar ke fama da shi.
Kamfanoni da hukumomin ba da hidima daga bangarori daban daban na kasar Nijeriya ne suka halarci taron kolin, inda suka tattauna makoma da kalubalen da za a fuskanta yayin da ake raya dangantakar dake tsakanin Nijeriya da Sin. (Zainab)