in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron liyafa ga daliban Najeriya da suka samu horo a Sin
2017-01-14 13:15:25 cri

Sashen cinikayya na ofishin jakadancin kasar Sin dake Najeriya a jiya Jumma'a,ya shirya wani taron liyafa ga wasu daliban Najeriya da suka koma gida, bayan samun horo a kasar Sin.

Mashawarcin ofishin mista Zhao Linxiang, da ministar kula da harkokin kasafin kudi da tsare-tsare ta kasar Zainab Ahmed, sun gabatar da jawabai, haka nan suma wakilan daliban sun yi nasu jawabi, kan zamansu a kasar Sin yayin da suke nazari da karatu.

A cikin jawabinsa, Zhao Linxiang ya ce, kasashen Sin da Najeriya na da makoma mai kyau wajen hadin kan tattalin arziki da cinikayya. Sannan aikin ba da horo ga 'yan Najeriya wani muhimmin kashi ne na huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu.

A ganinsa, daliban da suka samu horo, za su kasance gadar dake karfafa aminci tsakanin kasashen biyu, saboda haka, sashen cinikayya na ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, zai ci gaba da gudanar da ayyuka makamantan wannan, da nufin yaukaka dangantaka kan tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Nijeriya da Sin.

A na ta bangare, ministar kasafi da tsare-tsare ta Nijeriya, Zainab Ahmed ta yaba da shirin horon da gwamnatin kasar Sin ta samar wa Najeriya, tana mai fatan kasashen biyu za su kara samun damar yin cudanya da juna, inda ta kara da cewa, Nijeriya za ta iya koyon fasahohi daban – daban da kasar Sin ta yi amfani da su wajen samun bunkasa. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China