Lu ya bayyana cewa, a kwanan baya, gwamnatin Nijeriya ta yanke shawara a siyasance kan harkokin da suka saba wa manufar kasar Sin daya tak da hukumomin yankin Taiwan a kasar suka yi, tare kuma da daukar matakai. A wata sanarwar hadin gwiwa da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka fitar a jiya Laraba, gwamnatin Nijeriya ta nanata cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama babban tushe na kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare tsakaninta da Sin.
Dadin dadawa, Lu ya furta cewa, Sin ta nuna amincewa da babban yabo ga Nijeriya wajen martaba manufar kasar Sin daya tak. Kuma wannan ya sake nuna cewa, wannan manufa ta sami amincewa da karbuwa ga kowa da kowa.(Fatima)