A jiya Lahadi ne babban bankin kasar Sin ya ba da labarin cewa, ya yi maraba da kuma goyon bayan matakin sanya takardun lamunin kasar cikin tsarin hada-hada na kasa da kasa, lamarin da zai kara bayyana yadda kasuwannin takardun lamunin kasa da kasa suke gudana yadda ya kamata, kana zai taimakawa masu zuba jari na kasa da kasa su saya tare da sayar da takardun lamuninsu ba tare da wani shakku ba.
Mataimakin shugaban babban bankin kasar Sin Pan Gongsheng ya yi bayanin cewa, babban bankin kasar Sin ya kara bude kofar kasuwar takardun lamunin kasar ga kasashen ketare, inda ya goyi bayan kasashen waje da su sayar da takardun lamuninsu a kasar ta Sin. Kana kuma, babban bankin kasar Sin ya kara jawo hankalin masu zuba jarin ketare da su zuba jari a kasuwar takardun lamunin Sin. Babban bankin na Sin ya ce, nan gaba zai ci gaba da kyautata manufofin da suka dace, a kokarin kawo sauki da samar da muhalli mai kyau ga masu zuba jari na ketare.(Tasallah)