in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin: Jimillar GDP za ta kai 6.64% a bana
2017-02-23 13:09:43 cri

Jiya Laraba ne jami'ar Xiamen da jaridar da ke sharhi kan harkokin tattalin arziki karkashin shugabancin kamfanin dillancin labaru na Xinhua sun kaddamar da hasashensu a lokacin baraza na shekarar 2017, inda suka nuna cewa, idan kasar Sin ba ta sauya manufar kudinta ba a bana, watakila jimillar GDP da za ta samu a bana za ta kai kashi 6.64 cikin dari, kuma ana sa ran cewa, farashin kaya ba zai karu sosai ba, kuma ba zai yi wata raguwa ba a bana.

Rahoton hasashen da aka kaddamar jiya ya shaida cewa, ko da yake kasar Sin tana fuskantar babbar matsin lambar raguwar karuwar tattalin arziki a bana, da ma shekara mai zuwa, amma sakamakon zurfafa gyaren fuskar da ake yi kan sana'ar kera kaya, da fara kyautatuwar tsarin masana'antu, ya sa akwai alamar farfadowar sana'ar masana'antu. Sa'an nan kuma, sa'anar ba da hidima tana ta samun bunkasa sosai, lamarin da ya sassauta matsin lambar da ake fuskanta kan samar da isassun guraben aikin yi sakamakon raguwar karuwar tattalin arziki, kuma hakan ya taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin kasar. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China