in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar za ta mayar da hankali ga aikin daidaita tattalin arziki a shekarar 2017
2016-12-16 18:14:41 cri

Kasar Sin ta bayyana kudurinta na dora muhimmanci ga aikin daidaita tattalin arziki a shekarar 2017 mai kamawa. Wannan yana kunshe ne cikin wata sanarwar da aka fitar bayan kammala babban taron kara wa juna sani kan harkokin tattalin arzikin kasar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, yayin da ake kokarin neman ci gaba, gwamnatin za ta dora muhimmanci ga batun daidaita tattalin arziki a fannin tafiyar da harkokin gwamnati da dabarun aikin tafiyar da harkokin tattalin arziki. Haka kuma sanarwar ta ce, aiwatar da wadannan matakai, yana cikin batutuwan da aka baiwa muhimmanci a shekarar 2017 .

Har ila yau, sanarwar ta kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a fannin samar da kayayyaki a shekarar ta 2017. Kasar Sin na fatan samun gagarumin ci gaba a muhimman fannoni 5 ta fuskar yin gyare-gyare a bangaren samar da kayayyaki a shekara mai zuwa, ciki har da rage kayayyakin da ake samarwa fiye da kima, adana kayayyaki, rage kudaden da ake kashewa a fannin samar da kayayyaki da inganta sassan da suke da rauni da sauransu.

Kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace da ingantacciyar manufar kudi a shekarar 2107, wadanda za su kai cimma nasarar da ake fata a wannan fanni.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China